in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya yi kira ga kasashen Asiya da su kara hada kai da juna
2014-05-21 09:40:01 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya bayyana bukatar yin hadin gwiwa tsakanin kasashen Asiya, wajen tabbatar da hadin kai da dunkulewa waje guda, domin cimma burin bunkasar nahiyar Asiya.

Shugaban wanda ya gabatar da wannan bukata a jiya Talata, yayin wata liyafar karramawa da aka shiryawa mahalarta taron CICA na bana, ya kuma kara da cewa, Sin ta amince ta karbi bakuncin taron na wannan karo ne, bisa burin ta na tabbatar da zaman lafiya da lumana a nahiyar.

Kaza lika shugaban kasar ta Sin ya ce, kasarsa ta sha alwashin tabbatar da nasarar wannan taro, a matsayin gudummawarta, ga kudurin samar da daidaito, zaman lafiya da hadin kan nahiyar ta Asiya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China