in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin ya mika ta'aziyyarsa ga shugaban Lao bisa ga mutuwar manyan jami'an gwamnati
2014-05-19 09:59:45 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping a ranar Lahadin nan ya aike da sakon ta'aziyya zuwa ga shugaban kasar Lao Choummaly Sayasone bisa ga mutuwar mataimakin firaminista kuma ministan tsaron kasar Douangchay Phichit da wassu manyan jami'an gwamnati a hadarin jirgin sama.

Shugaba Xi a cikin sakon ya ce, manyan jami'an hudu da suka mutu cikin wannan hadari suna da muhimmanci ga kasar ta Lao wadanda suka ba da gaggarumar gudummuwa wajen gano da kuma fiddo da kasar a idon duniya, sannan suka ingiza dangantakar abokantaka da hadin gwiwwa tsakanin kasar Lao da kasar Sin.

Ya ce, wannan hadari ba ma kawai rashi ne ga kasar ta Lao ba, har ma ga abokantakar dake tsakanin kasar Sin da ita kanta Lao.

Wani jirgin soji dake dauke da manyan jami'an kasar na Lao ya fadi a gundumar Xieng Khouang dake arewa maso gabashin kasar a safiyar ranar Asabar, tare da hallaka mutane 16 dake cikin shi, ban da mutum daya kawai daya ya tsira. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China