Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan cikin jawabin sa na bude taron tattaunawa kan inganta cudanya, da karfafa hadin gwiwar nahiyar Asiya na CICA, karo na hudu da aka fara Larabar nan a birnin Shanghai, ya kara da cewa wajibi ne kasashen nahiyar su maida hankali ga batun tsaro ta hanyar hadin gwiwa, tare da daukar matakan magance rikice-rikice ta hanyoyin lumana.
Har ila yau shugaba Xi ya ce lokaci ya wuce da kasashen Asiya za su kafe wajen amfani da tsohon tunani na zaman doya da manja. Don haka ya ce dole ne a yayata bukatar aiwatar da hadin gwiwa, game da wanzar da tsaron nahiyar cikin dogon lokaci.
Shugaban kasar ta Sin wanda ya bayyana taron CICA a matsayin taro mafi girma, da ke bada damar tattauna batutuwan da suka jibanci tsaron shiyyar, ya kara da cewa akwai bukatar fadada hadin gwiwar CICA, da sauran hukumomi da cibiyoyin da ba na gwamnati ba, domin cimma kudurorin taron ta fuskar inganta tsaro.
Bugu da kari shugaban kasar ta Sin ya ce kasar sa za ta sauke nauyin dake wuyan ta na jagorancin taron na bana, ta hanyar yin aiki kafada-da-kafada da sauran kasashen nahiyar, wajen daukaka matsayin harkar tsaron nahiyar zuwa matsayi na gaba. (Saminu)