A ran 23 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi shawarwari da takwaransa na Iraki Hoshyar Zebari, bayan hakan, ya gaya wa manema labarai cewa, a ranar Asabar 22 ga wata, kwamitin sulhu ya zartas da kuduri mai lambar 2139 kan batun jin kai na Sham bisa dukkan kuri'un amincewa, wanda ya nuna niyyar kasashen duniya da ra'ayi daya da suka samu wajen daidaita matsalar jin kai ta kasar Sham tun da wuri, wannan dai ya sanar da muhimman ci gaban da aka samu wajen daidaita matsalar Sham ta hanyar siyasa, game da haka, Sin ta nuna goyon baya da maraba.
Mista Wang ya ce, har kullum Sin tana dukufa wajen ganin an saukaka matsalar jin kai a kasar Sham, kuma ta dade tana ba da taimakon jin kai ga jama'ar kasar Sham da masu gudun hijirar kasar a kasashen waje. Ya cigaba da cewa, a yunkurin duba kuduri mai lambar 2139, Sin tana daukar matsayi mai yakini, sannan bisa adalci ta shiga tsakani a bangarori daban daban don gani an kau da bambancin ra'ayi da kara samun ra'ayi daya, kuma Sin ta taimaka ganin an zartas da kudurin.
Wang Yi ya kara da cewa, Sin tana bukatar bangarorin dake arangama da juna a kasar Sham da su yi amfani da wannan dama, su aiwatar da kuduri mai lambar 2139, su tsagaita bude wuta da nuna karfin tuwo, su kuma bi hanyar shawarwari, don rage bambancin ra'ayi, da kara amincewar juna, ta yadda za a warware matsalar Sham a siyasance cikin lokaci kuma kasar Sin za ta ci gaba da ba da taimakonta. (Danladi)