Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Madam Hua Chunyin wadda ta bayyana matsayin kasar a gun taron manema labarai da aka yi a Litinin din 17 ga wata ta lura cewa, rikicin kasar sham yana shafar matsaloli da bambancin ra'ayi da dama, abin da ya kara tabarbare halin da ake ciki.
Ta ce shawarwarin da aka yi a Geneva ya kasance shawarwarin da ya kamata a yi a kai a kai da yake bukatar bangarorin biyu su amince da juna a lokacin ganawarsu domin a fidda wata hanya da ta dace wajen cimma matsaya daya, don haka ba za'a iya warware wannan batu ta kiran taro sau daya ko biyu kawai ba.
Rahotanni na nuna cewa an kammala shawarwarin kasa da kasa a zagaye na biyu kan rikicin kasar Sham a 15 ga wata ba tare da samun wani cigaba ba, inda bangarorin biyu ba su tabbatar da lokacin da za'a yi shawarwari mai zuwa ba, sai dai an cimma matsaya kan batun da za a tattauna nan gaba. (Amina)