Idan ba a manta ba,a shekarar 1954 ne kasashen Sin, Indiya, Myammar suka gabatar da wadannan ka'idoji biyar cikin hadin kai,inda suka yi alkawarin mutunta ikon mulki da cikakkun yankunan juna, bai kamata wani ya kai hari ko tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran kasashe ba, har ma a mori juna da zama tare cikin lumana.
Mr Liu ya jaddada cewa, a matsayin kasar dake daukar nauyin dake wuyanta, Sin za ta ci gaba da aiwatar da wadannan ka'idoji tare kuma da kare ikon mulkin kasa da kiyaye zaman lafiya da tsaron duniya baki daya, har ma da sa kaimi ga hadin kai da bunkasuwar tattalin arziki, sannan da martaba tsare-tsare da dokokin duniya.
Ban da haka kuma, yayin da ya tabo maganar tekun kudancin Sin, Mr Liu ya ce, Sin za ta ci gaba da sa kaimi ga kasashen da wannan batu ya shafa da su yi shawarwari domin warware wannan matsala, bai kamata sauran kasashe su rika aza ayar tambaya kan niyyar da Sin take yi na kiyaye zaman karko a wannan yanki ba. (Amina)