Firaministan Sin ya ba da umurnin kama wadanda suka kai harin Urumqi
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya amsar da ta dace kan mummunan harin da wasu maharan suka kai a kasuwar Urumqi dake jihar Xinjiang mai cin gashin kanta da safiyar Alhamis din nan, inda ya bayyana cewa, ya kamata a kula da wadanda suka jikkata a wannan hari yadda ya kamata, a sa'i daya kuma, a gano wadanda suka kai harin, don kama su ba tare da bata lokaci ba. Ya kuma kara da cewa, ya kamata a ci gaba da karfafa ayyukan tsaro, don yin rigakafi kan tagwayen al'amura, da kuma kawar da yanayin tashin hankali a zaman takewar al'umma, ta yadda za a iya kiyaye rayuka da dukiyoyin al'umma tare da shimfida zaman karko a yanayin zaman takewar al'umma. (Maryam)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku