Bincike ya nuna cewa, sama da kashi 70 cikin 100 na kamfanonin da aka yi musu bincike, sun bayyana cewa, yawan kayayyakin da za su fitar a karshen rabin shekarar bana, zai karu.
Haka kuma, masu sayar da komfuta, na'urorin sadarwa, da kayayyakin tsaro sun fi nuna farin ciki wajen fitar da kayayyakinsu, an kuma yi hasashe cewa, kashi 81 cikin 100 na kamfanonin sun bayyana cewa, za su samu karin ribar fiye da yadda suke zato. Ribar da kasashe masu saurin bunkasuwar tattalin arziki suke samu ta zama babbar hujjar da aka yi amfani da ita ga yin wannan hasashe, ban da wannan kuma, kasashen da ke Latin Amurka da kungiyar AU da ta EU da yankunan Asiya da tekun Fasific za su ci gaba da samar da babbar damar yin ciniki ga kasar Sin.(Bako)