in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi alla wadai da harin ta'addanci a kasar Sin
2014-05-24 15:57:18 cri
Shugabar kwamitin kungiyar tarayyar Afrika AU, madam Nkosazana Dlamini Zuma ta yi allawadai da harin ta'addancin da aka kai a ranar Alhamis wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 39 tare da jikkata mutane da dama a yankin jihar Xinjiang ta Ouigoure mai cin gashin kanta dake arewa maso yammacin kasar Sin, in ji kungiyar AU a cikin wata sanarwar da ta fitar a ranar Jumma'a.

Madam Dlamini Zuma ta yi kira ga gamayyar kasa da kasa da ta dauki matakai cikin hadin kai domin yaki da hare-haren ta'addanci dake karuwa a duniya, da kuma tashi tsaye wajen kawar da wannan annoba a cikin sanarwar, haka kuma jami'ar ta tunatar da cewa barazanar ta'addanci da masu kaifin kishin addini, na janyo ma duniya babbar matsala, hakan na nuna cewa ya zama dole a ci gaba da samun hadin kasa da kasa daga dukkan fannoni domin karfafa karfin yaki da wannan bala'i a duniya baki daya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China