in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasar Sin sun taya Jacob Zuma murnar nasarar babban zabe a kasar Afirka ta Kudu
2014-05-22 15:21:15 cri

A ranar Alhamis 22 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika da wasikar taya murna ga Jacob Zuma, bisa nasarar da ya samu a babban zaben shugaban kasar Afirka ta Kudu.

A cikin wasikar, shugaba Xi ya bayyana cewa, a cikin shekaru biyar da suka gabata, gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta samu sabbin nasarori wajen gudanar da harkokin kasa da samun bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma bisa shugabancin Zuma. A wannan karo, Jam'iyyar ANC ta sake samun nasarar babban zaben, sannan shugaba Zuma shi ma ya samu nasarar cigaba a kan mukamin shugaban kasar, abin da ke sheda amincewar da jama'ar kasar suka nuna musu.

A wannan rana kuma, shi ma firaministan kasar Sin Li Keqiang ya buga waya ga shugaba Zuma don taya shi murnar sake mayewa kujerar shugabancin kasar. Inda Li ya bayyana cewa, kasashen Sin da Afirka ta Kudu dukkansu muhimman kasashe ne masu tasowa, sannan kuma akwai dankon zumunci a tsakaninsu, bugu da kari sun samu kyawawan sakamako wajen cudanya da hadin kansu. Ya ce inganta hadin kan kasashen biyu a kan aminci ya dace da babbar moriyar jama'arsu, zai kuma taimaka wajen samun zaman lafiya da ci gaban duniya baki daya.

Firaminista Li daga nan sai ya bayyana bukatar da ke akwai na yin kokari tare da shugaba Zuma don ciyar da hadin kan kasashen biyu zuwa gaba, da kuma zaburad da sabon jini ga dangantakar abokantaka a tsakanin Sin da Afirka ta Kudu bisa manyan tsare-tsare.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China