Bisa labarin da aka bayar, an ce, burin bikin shi ne fara hadin gwiwa a fannoni uku, wato hadin gwiwa a tsakanin kamfanoni da hukumomin gwamnatocin kasashen Afirka, da tsakanin kamfanoni da masu sayen kaya na kasashen waje, da kuma tsakanin kamfanonin kasar Sin da kamfanonin kasashen Afirka. A gun bikin, za a yi kokarin kara yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannonin albarkatun ma'adinai, gina ababen more rayuwa, da kera na'urori, sadarwa, aikin gona, yawon shakatawa da dai saurausu. (Zainab)