in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban babban taron kwamitin kula da kayan tarihi ya taya kasar Sin murnar samun sabbin kayayyakin tarihi guda biyu
2013-06-25 10:45:26 cri
Jiya Litinin 24 ga wata ne shugaban taron kwamitin kula da kayan tarihi na duniya karo na 37, kuma mataimakin firaministan kasar Cambodia, Sok An ya taya kasar Sin murnar samun nasarar sabbin kayayyakin tarihi na duniya guda biyu.

A yayin taron manema labaru da aka shirya a Phnom Penh, babban birnin kasar Cambodia, Sok An ya yi bayani kan nasarori, da ci gaba da aka samu a yayin babban taron, inda ya ce, ya taba kai ziyara wasu shahararrun wuraren tarihi na duniya dake kasar Sin, kuma a kowace ziyara ya kan gano cewa, lallai gwamnatin kasar Sin da jama'arta, na mayar da hankali sosai wajen kiyaye wadannan muhimman abubuwa masu daraja na al'ummar kasar.

Dutsen Tianshan na jihar Xinjiang, da kunyar Hani ta lardin Yunnan, na ciki jerin wuraren tarihi da suka shiga wannan jadawali kan muhimman kayan tarihi na duniya a wannan karo.

Sok An ya ce, kasar Sin na da kayayyakin tarihi na duniya guda 45, wadda hakan ya sanya ta zama babbar kasa ta biyu a duniya, wajen adana kayayyakin tarihi. Daga nan sai ya yi godiya ga aikin kiyayen wadannan kayayyakin tarihi da kasar ke yi.

Babban taron kayayyakin tarihi dai taro ne na shekara shekara da kwamitin kula da kayayyakin tarihi na duniya karkashin hukumar UNESCO ke shiryawa. An kuma bude babban taron a wannan karo ne tun ranar 16 ga wata a birnin Phnom Penh, ana kuma fatan rufe shi a ranar 27 ga wata a birnin Siem Reap, wurin da gidan ibada na Angkor Wat, dake kasar ta Cambodia yake. Bisa kudurin da aka yanke yayin babban taron, za a shirya babban taron kwamitin karo na 38 a kasar Qatar. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China