in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana goyon bayan Najeriya a yakin da take yi da ta'addanci
2014-05-21 20:25:07 cri
Kasar Sin ta bayyana goyon bayanta kan matakan da Najeriya ke dauka na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai jawabi game da tagwayen hare-haren bam din da aka kai ranar Talata a garin Jos, babban birnin jihar Filato na Najeriya, harin da ya haddasa mutuwar mutane 162 ya zuwa yanzu tare da jikkata mutane da dama.

Hong Lei ya ce, kasar Sin tana goyon bayan matakan da Najeriya take dauka na tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a kasar.

Ya ce kasar Sin a shirye take ta hada hannu da kasashen duniya wajen taka muhimmiyar rawa a yunkurin da ake yi na yaki da ayyukan ta'addanci tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar Afirka. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China