in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan kara ba da gudummawa wajen bunkasa nahiyar Afirka
2013-05-27 20:33:32 cri
A ranar Litinin 27 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, Hong Lei ya bayyana a gun taron 'yan jaridu cewa, Sin na fatan hada kai tare da kasashen Afirka, da zummar sa kaimi ga bunkasa sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da kasashen Afirka, tare da kara ba da gudummawa ga bunkasa nahiyar yadda ya kamata.

Hong ya bayyana cewa, taron kolin musamman na murnar cika shekaru 50 da kafa kungiyar AU na da muhimmanci sosai, tare da cimma babbar nasara. Sin ta yi imani cewa, bisa wannan zarafi, kasashen Afirka za su kara farfado da tunanin yaki da nuna bambanci ga launin fata da na bunkasa nahiyar Afirka, tare da kara hada kansu wuri daya, a kokarin samun sabuwar nasara a fannin sa kaimi ga raya kasashen Afirka da kansu da kuma neman samun ci gaba tare.

Haka kuma Hong ya jaddada cewa, Sin tana dora muhimmanci sosai kan bunkasa dangantaka tsakaninta da kasashen Afirka. Idan ba'a manta ba a watan Maris na wannan shekara, shugaban kasar Xi Jinping ya zabi nahiyar Afirka a matsayin inda ya fara kai ziyararsa ta farko bayan darewarsa wannan kujera. A wannan karo kuma, ya aika da sakon murna ga taron kolin na AU, ta hannun mataimakin firaministan kasar Sin, Wang Yang wanda ya halarci taron. Wannan ya nuna cewa, Sin na dora muhimmanci sosai kan dangantakar abokantaka tsakaninsu, kuma dukkansu aminai ne.

Don haka Sin na fatan yin kokari tare da kasashen Afirka, da aiwatar da sakamakon ziyarar shugaba Xi a nahiyar Afirka, da kara amincewa da juna, da karfafa hadin gwiwa tsakaninsu a duk fannoni, da sa kaimi ga bunkasa sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu, ta yadda za ta kara ba da gudummawa ga bunkasa nahiyar Afirka.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China