Kasar Sin da hukumar lafiya ta WHO, tare da ma'aikatar kiwon lafiya ta yankin Zanzibar na kasar Tanzania, sun daddale jarjejeniyar shawo kan cutar tsotsewar jini da a turance ake kira Schistosomiasis.
A safiyar Laraba 21 ga watan nan na Mayu ne dai, mataimakin shugaban kwamitin kula da kiwon lafiya da haihuwa na kasar Sin Wang Guoqiang, wanda ke halartar babban taro na 67 na kiwon lafiya a birnin Geneva, da babbar daraktar hukumar WHO Margaret Chan, da kuma ministan kiwon lafiya na yankin Zanzibar a kasar Tanzania Juma Duni Haji, suka daddale yarjejeniyar ta yankin Zanzibar.
Bayan kammalar bikin sanya hannu kan takardar, Wang Guoqiang, da ministan kiwon lafiya na yankin Zanzibar sun zanta da manema labarai, inda Mr. Wang ya bayyana cewa, kasar Sin ta hada kai da WHO, da Zanzibar, wajen shawo kan cutar tsotsewar jinin ne, bisa kudurin da firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatar, na ba da taimako ga bukatun Afirka, da bunkasa amincewar juna, gami da burin inganta hadin kai.
Kaza lika, wannan aiki ya zama irin sa na farko da kasar Sin ta hada kai tare da kungiyar kasashen duniya, wajen baiwa kasashen Afirka tallafi ta wannan fuska. Kana muhimmin aiki ne da za a gudanar don aiwatar da "Sanarwar Beijing", wadda aka cimma a shekara ta 2013, a yayin taron ministoci na hadin gwiwar Sin da Afirka ta fuskar kiwon lafiya, wanda ya tanaji taka muhimmiyar rawa, wajen kyautata aikin tallafawa Afirka da kasar Sin ke yi ta fuskar kiwon lafiya, da neman samun sabbin hanyoyin hadin gwiwar kasa da kasa, don taimakawa nahiyar ta Afirka a wannan fanni. (Kande Gao)