Yayin ganawar, shugabannin 2 sun nuna gamsuwa kan yadda ake kokarin inganta huldar dake tsakanin bangarorin 2, gami da daukar niyyar kara yin hadin gwiwa, don ciyar da wannan huldar hadin kai da ta shafi manyan tsare-tsaren kasashen 2 zuwa gaba.
A cikin jawabin da ya gabatar, shugaba Xi Jinping ya ce, kasashen Sin da Rasha aminai ne dake makwabtaka da juna, wadanda ke taka muhimmiyar rawa a dandalin kasa da kasa. Saboda haka, kokarin kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2 ya dace da bukatar kiyaye zaman lafiya da nuna adalci a duniya, gami da bukatun kasashen 2 na samun walwala.
A nasa bangaren, shugaba Putin na kasar Rasha ya ce, an shiga cikin wani sabon yanayi na samun saurin ci gaban huldar dake tsakanin kasashen 2, ganin yadda ake gudanar da tsarin hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin kasashen 2 lami lafiya, tare da cimma nasarori da yawa kan cudanyar da ake yi a fannoni daban daban.
Bayan ganawar tasu, shugabannin 2 sun sa hannu kan wata sanarwar da ta bayyana sabon yanayin da ake ciki na kokarin inganta hadin gwiwar bangarorin 2, daga bisani sun gane wa idonsu yadda aka kulla yarjejeniyoyin da suka shafi masana'antu, zirga-zirga, sadarwa, da sauran fannoni da dama. (Bello Wang)