in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Rasha za ta sayar wa kasar Sin iskar gas
2014-05-21 19:33:55 cri
A yau Laraba 21 ga wata a birnin Shanghai na kasar Sin, kasashen Sin da Rasha sun sa hannu kan wata takardar kara fahimtar juna da wata kwangila kan yadda kasar Rasha za ta sayar wa kasar Sin iskar gas da za a iya sufurinsa ta bututun iskar gas din dake yankunan gabashin kasashen biyu. Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Rasha Vladimir Putin sun halarci bikin sa hannu kan wadannan muhimman takardu biyu na yin hadin gwiwa a fannin makamashi tsakanin kasashen Sin da Rasha.

Bisa kwangilar da aka kulla yau, kasar Rasha za ta sayar wa kasar Sin iskar gas da yawansa zai kai kubik mita biliyan 38 a kowace shekara tun daga shekarar ta 2018 ta bututun da za a shimfida a yankunan dake gabashin kasashen biyu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China