A wannan rana, a yayin taron manema labaran da aka saba yi a fadar MDD dake birnin Geneva, kakakin ofishin kula da harkokin jin kai na MDD ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2011, musayar wuta tsakanin sojojin gwamnatin kasar da dakarun wasu kungiyoyi a lardin Katanga na ci gaba da tsananta, lamarin da ya haddasa babbar illar kai tsaye ga mazaunen wurin, amma ba a taba gabatar da halin da wadannan mazaunen wurin suke ciki ga kasashen duniya ba. Cikin shekarar da ta gabata, an sha fama da fyade, yin garkuwa, shigar da yara cikin yake yake da sauran mummunan ayyuka a wurin.
Kakakin ya kuma kara da cewa, har yanzu akwai kungiyoyin jin kai kimanin guda 50 da suka hada da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, hukumar tsara shirin abinci ta duniya da kuma kwamitin Red Cross na kasashen duniya da dai sauransu dake dukufa wajen ba da taimakon jin kai a wurin, amma ba su iya gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, sakamakon tabarbarewar yanayin tsaro a yankin da kuma karancin kudade.(Maryam)