in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU na damuwa sosai game da tabarbarewar matsalar tsaro a gabashin RDC-Congo
2013-09-01 16:05:50 cri
Kungiyar tarayyar Afrika AU ta bayyana a ranar Asabar cewa tana cikin damuwa sosai kan tabarbarewar yanayin tsaro a gabashin kasar RDC-Congo. A cikin wata sanarwar da aka bayar a birnin Addis Abeba na kasar Habasha, kwamitin tsaro na AU ya yi tir da allawadai kan sake barkewar tashe tashen hankali daga wajen 'yan tawayen M23 da suka haddasa asarar rayukan fararen hula da kuma lalata dukiyoyi a cikin yankunan da 'yan tawayen suka mamaye da birnin Goma. Gamayyar Afrikar ta yi kira ga 'yan tawayen M23 dasu kawo karshen duk wasu ayyukan soja ta yadda za'a iya cimma wani sulhun siyasa mai karko game da wannan rikici bisa tsarin yarjejeniyar Kampala, in ji wannan sanarwa. Kungiyar AU ta jaddada cewa 'yan tawayen M23 da kuma kungiyoyi masu makamai za su kasance masu laifi kan duk wasu ayyukan keta hakkin dan adam a cikin yankunan dake karkashin mallakarsu. Haka kuma AU ta nuna yabo kan kokarin shugaban kasar Congo Denis Sassou Nguesso yake na taimakawa jituwa da fahimtar juna tsakanin shugabannin wannan shiyya tare da ba shi karfin gwiwa na cigaba da wannan kokari nasa in ji wannan sanarwa. Daga karshe AU ta yi kira ga kasashen wannan shiyya da su kara karfafa kokarinsu domin warware wadannan matsaloli ta yadda za'a iya karfafa cigaban da aka samu a shekarun baya. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China