in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci DRC da ta kawo karshen bazuwar farmakin fyade
2014-04-10 16:49:29 cri
A ranar Laraba ne jami'an majalisar dinkin duniya suka gabatar da kira a kan gwamnatin jamhuriyar dimokuradiyya ta Congo-DRC da ta dauki takobi na yaki da yawaitar hari na yi wa mata fyade.

Babbar kwamishinar tabbatar da 'yancin bil'adama ta majalisar dinkin duniya , Navi Pillay, ta ce a halin da ake ciki jamhuriya dimokuradiyyar ta Congo, ba ta dauki wani mataki domin hukunta wadanda suka aikata irin wadannan laifukan, duk da nasarar da ake samu wajen tilastawa wadanda suka yi fyaden amsa laifinsu.

Pillay ta gabatar da kira a kan gwamnatin da ta ba da fifiko wajen yaki da fyade wanda ake yi kara-zube, tare da gudanar da cikakken bincike nan take da an aikata laifin.

Pillay ta kuma bukaci da a hukunta wadanda ake zargi da laifin aikata fyaden da wadanda ake zargin sun ba da umurnin da a aiwatar da irin wannan laifi.

Wannan kira da Pillay ta yi ya zo daidai da lokacin da ofishin majalisar dinkin duniya dake jamhuriyar dimokuradiyyar ta Congo ya gabatar da wani cikakken rahoto, wanda ya nuna cewar adadin rajistar wadanda fyaden ya shafa a Congon Kinshasha ya kai dubu 3 da dari 6, tun daga watan Janairu na shekara ta 2010, zuwa Disambar shekara 2013.

Karamar sakatare-janar mai gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya na majalisar dinkin duniya Herve Ladsous ta ce ya kamata gwamnatin ta Congo da ta dauki mataki a kan gudanar da cikakken binciken dalilan aikata laifuka na fyade tare da magance matsalar. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China