in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 102 sun rasu a sanadiyar rikice-rikicen da suka faru a wasu sassan Congo(Kinshasa)
2014-01-01 20:14:52 cri
Gwamnatin kasar Congo(Kinshasa) ta ba da rahoto a jiya Talata 31 ga watan Disamba na shekarar 2013 cewa, mutane 102 ne suka rasa rayukansu a sanadiyar rikice-rikicen da suka faru a wasu sassan kasar, kana wasu 94 daga cikinsu mahara ne, har yanzu, bisa rahoton da aka samu, an ce, babu fararen hula da suka rasu cikin rikice-rikicen.

Ministan harkokin watsa labaru na kasar, Lambert Mende Omalanga ya ce, ya zuwa yanzu ba a san asalin wadanda suka kai farmakin ba, ko da ya ke ba juyin mulki suka yi niyyar yi ba, illa su tsorata jama'ar kasar. Sa'an nan kuma, za a gabatar da wannan batu a cikin harkokin shari'ar kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China