in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana zaman dar dar bayan barkewar sabon rikici a Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo
2013-10-26 17:18:19 cri
Rahotanni daga janhuriyar dimokaradiyyar Congo sun tabbatar da barkewar wani rikici a gabashin kasar a ranar Jumma'a 25 ga wata.

Kakakin babban magatakardar MDD Martin Nesirky ne ya bayyanawa manema labaru hakan, yayin taron ganawa da 'yan jaridun na wannan rana, Nesirky ya ce rikicin ya barke ne tsakanin dakarun kungiyar nan ta M23, da sojojin kasar Congo, a wani wuri dake kusa da Kibumba, mai nisan kilomita 15 daga birnin Goma. Nesirky ya ce an yi amfani da manyan bindigogi da igwa yayin dauki ba dadin da ya tilasawa wasu al'ummun yankin su kimanin 5,000 tsallaka iyakar kasar zuwa Rwanda.

Ya ce tuni tawagar MDDr ta gudanar da sintiri da jiragen sama, domin tantance yanayin da ake ciki a yankin.

Tun dai cikin watan Afrilun shekarar da ta gabata ne kungiyar M23 ta fara ta da kayar baya, musamman ma a yankunan dake gabashin kasar, lamarin da ya kai ga kwace birnin Goma na wani dan lokaci, kafin fitar da su daga birnin, sakamakon matsin lambar kasahen duniya dake da burin tabbatar da kyakkyawan yanayin zaman lafiya a kasar.

Yunkurin da mahukuntan kasar Uganda suka sha yi na shiga tsakani, na ci gaba da fuskantar koma baya, tun bayan fara zaman tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki a watan Disambar bara. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China