A cikin sakon shi Shugaba Xi ya bayyana cewa, an cigaba da huldar ta diplomasiyya tsakanin Sin da Congo-Brazzaville cikin shekaru 50 da suka wuce abin da ya ce ya kawo bunkasuwa, kuma dangantaka tsakanin kasashen biyu ta kai wani sabon yanayi mai kyau. Shugaban kasar na Sin
Ya lura da cewa sada zumunci tsakanin jama'ar Sin da Congo-Brazzaville, da yin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ya dace da bukatar bunkasuwa, tare da goyon bayan juna wajen cimma burin neman samun ci gaba. A don haka in ji shi Sin na fatan kara hadin gwiwa da sada zumunci tsakanin kasashen biyu, da sa kaimi ga zurfafa dangantaka tsakaninsu, a kokarin kara kawo alheri ga Sin da Congo-Brazzaville da kuma jama'arsu baki daya.
A nasa bangare, shugaba Denis Sassou-N'guesso ya bayyana cewa, cikin shekaru 50 da suka gabata, kasashen biyu sun yi mu'amala da juna sosai, da hada kai da taimakawa juna, tare da samun sakamako mai kyau. Da haka dangantaka tsakanin Congo-Brazzaville da Sin ta zama abin koyi a fannin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa.
Ya kara da cewa, a cikin 'yan shekarun da suka wuce, a karkashin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, hadin gwiwa tsakanin kasashen 2 ya kyautata rayuwar jama'ar Congo-Brazzaville, tare da kawo babbar sauyi a fannoni da dama na kasar.(Fatima)