Kakakin ofishin MDDr Martin Nesirky ne ya tabbatar da hakan, yayin ganawar sa da 'yan jaridu. Nesirky ya kara da cewa ana sa ran amfani da wannan jirgin sama ne domin ba da kariya ga fararen hula dake yankunan gabashin kasar masu fama da yawan tashe-tsahen hankula.
Manyan jami'an MDD, ciki hadda karamin sakatare mai lura da harkokin wanzar da zaman lafiya a kasar Herve Ladsous, da wakilin babban magatakardar MDD a kasar Martin Kobler, sun halarci bikin kaddamar da wannan jirgi.
Da yake jawabi bayan kaddamar da harba jirgin Mr. Ladsous ya ce wannan ne karon farko da ofishin MDD zai yi amfani da irin wannan jirgi domin aikin wanzar da zaman lafiya, wanda kuma zai yi matukar tallafawa aikin da tawagar MONUSCO ke yi, musamman ma wajen karade dukkanin sassan da ake bukatar sanya ido kan su.
A baya bayan nan dai dakarun sojin kasar Congo, da hadin gwiwar tawagar ta MONUSCO sun samu nasarar karya lagon kungiyar 'yan tawaye kasar ta M23, wadda a baya ta mamaye lardin Arewacin Kivu, matakin da ya tilasa M23r ajiye makamai. (Saminu Alhassan)