in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kusan kwantar da kurar da ta tashi a birnin Kinshasa
2013-12-30 21:19:38 cri
Rahotanni daga Kinshaha,fadar mulkin kasar Jamhuriyar Dimokuraddiyar Congo,na cewa an kusa kawo karshen fadan da ya barke a safiyar ranar Litinin, kana gwamnati ta shawo kan lamarin.

Wata majiyar gwamnatin kasar ta ce an kashe a kalla mahara 40 wadanda suka yi musayar wuta da sojojin gwamnati a birnin.

Rahotanni na baya bayan nan sun ce wasu maharan sun yi garkuwa da mutane a gidan telabijin na kasar Congo TRNC, kana sun kai hari ga filin saukar jiragen sama, da kuma hedkwatar sojojin kasar. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China