Taimakon jin kan ya hada da katifu 900, abinci kusan ton goma da kuma barguna fiye da 2000, in ji manjo janar Tim Mukunto, wani babban jami'in rundunar sojojin kasar ta takwas FARDC, tare da bayyana cewa wannan taimako ya zo domin kara wa bisa kokarin da gwamnatin kasar take bisa tsarin ba da kulawa ga tsoffin mayaka bisa yarjejeniyar karbe makamai ta Congo Kinshasa.
MONUSCO da kungiyoyin MDD dake kasar Congo Kinshasa sun nuna damuwa kan halin zaman rayuwa na wadannan tsoffin 'yan tawaye dake sansanin Bweremana da aka kiyasta yawansu zuwa fiye da 11,140 inda aka hada 2,600 na tsoffin mayakan kungiyoyin masu makamai da suka fito daga kasashen waje da aka tsugunar dasu zuwa yankuna uku Kitona a gundumar Bas-Congo, Kamina a yankin Katanga da kuma Kotakoli a yankin Equateur. (Maman Ada)