Amfani da wadannan na'urori zai taimakawa sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD dake kasar Congo Kinshasa sanya ido kan fice de shigen dakaru masu makamai da kuma kare fararen hula yadda ya kamata a cikin wannan shiyya. Haka kuma jami'in ya kara da cewa wadannan jirage masu sarrafa kansu na MDD basu dauke da makamai.
A halin yanzu, mista Nesirky ya bayyana cewa ma'aikatar dake kula da harkokin tabbatar da zaman lafiya ta MDD na iyar tabbatar cewa ana kan matakin karshe na samun wadannan jiragen sama. Kuma kamfanin da zai samar da wadannan jiragen shi ne kamfanin SELEX ES na kasar Italiya in ji kakakin na MDD.
Tawagar MDD, ta jibge sojojin dubu goma sha bakwai, adadi mafi yawa na sojojinta a duniya dake gabashin Congo Kinshasa tun shekaru da dama da suka gabata. Kasar na fama da hare haren 'yan tawayen M23 a yankin iyakarta da kasashen Rwanda da Uganda tun daga shekarar bara. (Maman Ada)