in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD na nuna damuwarta sosai kan sake barkewar yake yake a gabashin RDC-Congo
2013-10-27 16:40:16 cri
Wakiliyar musamman ta sakatare janar na MDD game da yankin Grand Lakes, madam Mary Robisnson da kuma manzon musamman na sakatare janar na MDD a kasar RDC-Congo, mista Martin Kobler sun bayyana matukar damuwarsu kan cigaban tashe tashen hankali a gabashin wannan kasa.

A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya ruwaito a ranar Asabar, jami'an biyu sun yi kira ga dukkan bangarorin da wannan rikici ya shafa da su dakatar da bude wuta tsakaninsu tare da komawa teburin shawarwari a birnin Kampala.

Haka kuma suna kira ga bangarorin da su gabatar da rahotonnin da suka shafi rikice rikicen sojoji ga kwamitin sa ido na hadin gwiwa domin baiwa kwamitin damar gunadar da binciken da ya dace, da kuma bada hadin gwiwarsu sosai ga wannan tsari a kai a kai ta yadda za'a gano gaskiyar abubuwan da suka faru in ji madam Robinson da mista Kobler.

Ya zama wajibi bangarorin dake halartar shawarwarin su cimma wata yarjejeniya nan take kan sauran batutuwan dake kan tebur a Kampala in ji jami'an biyu.

'Yan tawayen M23 suna cikin tattaunawa tare da gwamnatin RDC-Congo a kasar Uganda. Da suke fuskantar matsin lamba a cikin watan Mayun shekarar 2012 a yankin arewacin Kivu, 'yan tawayen M23 sun bukaci da aiwatar da yarjejeniyar ranar 23 ga watan Maris da aka cimma a shekarar 2009 tsakanin gwamnati da gungun kungiyoyin dake rike da makamai.

Kusan yankuna da dama tare da kauyukan dake arewacin Kivu ne suke a karkashin 'yan tawayen M23. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China