A yayin wannan taron shekara-shekara, ministocin kiwon lafiya na kasashe mambobi 47 na kungiyar OMS na shiyyar Afrika za su tattauna muhimman batutuwa dake cikin jadawalin wannan taro, musammun ma kan jadawalin aiki na shekarar 2012 na darektan shiyya na kungiyar OMS kan ayyukan kungiyar a nahiyar Afrika, tsufa cikin koshin lafiya a Afrika, kalubalen kiwon lafiyar mata a Afrika, karfafa matsayin likitar gargajiya a cikin tsarin kiwon lafiya.
A cewar reshen kungiyar OMS bangaren Afrika dake Brazaville, mahalarta wannan taro za su mai da hankali kuma kan karfafa kwarewa wajen daidaita magunguna da kayayyakin kiwon lafiya a shiyyar Afrika, da sakamakon da aka samu wajen aiwatar da tsarin shiyya kan yin allura da sauran manyan batutuwa a wannan fanni.
A cikin manyan jami'an da za su halarci wannan taro karo na 63 akwai darektar janar ta kungiyar OMS, dokta Margaret Chan, darektan shiyya na OMS, dokta Luis Gomes Sambo, manyan jami'an kungiyar OMS da na reshen shiyyar Afrika, wakilan ressan kungiyon kiwon lafiya na MDD, wakilan kungiyoyin kasa da kasa dana kungiyoyi masu zaman kansu. (Maman Ada)