A wannan rana, kakakin gwamnatin kasar Lambert Mende ya bayyana cewa, babu shakka harbar da kungiyar M23 ta yi a kan jirgin saman kungiyar MONUC ta saba da dokar kasa da kasa, kuma bisa ka'idojin yarjejeniyar Geneva da karin bayaninta, ana iya yanke mata hukuncin laifin yaki. Don haka Mr. Mende ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da ta dauki matakin da ya wajaba domin kiyaye matsayin MDD.
Ran 12 ga wata, kungiyar adawa ta M23 ya amince da daukar alhakin harbo wani jirgin sama mai saukar ungulu na kungiyar MONUC bisa dalilin cewa, wannan jirgin sama bai bi hanyar da ta dace ba. Amma Mr. Mende ya ce, DRC ba ta hana jiragen saman kungiyar MONUC su shiga cikin sararin saman kasar ba. (Maryam)




