Wasu kananan kotunan al'umma da ke yankin jihar Xin Jiang mai cin gashin kanta sun yi zama inda suka yanke hukunci kan laifufuka 16 da aka aikata na watsa wasu hotunan bidiyo da ke iya tayar da hankula a kwanan baya.
Babbar kotun ta kira taron manema labaru a ran 21 ga wata, inda ta bayyana cewa, wadannan laifufuka da aka aikata sun shafi shiryawa da ba da jagoranci ga ayyukan ta'addanci, rura wutar bambanci tsakanin kabilu, da kera bindigogi ba bisa doka ba, kuma an yankewa wadannan mutane 39 hukunci, inda aka yankewa wasu daga cikinsu daurin shekaru 15. (Amina)