A cewar ofishin daya daga cikin mambobin kungiyar ta ETIM mai suna Isma'il Yusup ne ya kitsa yadda za a kaddamar da harin a wajen kasar a ranar 22 ga watan Afrilun da ya shude, inda ya umarci wasu magoya bayan kungiyar su 10 da kaddamar da harin.
Idan dai za a iya tunawa da maharan sun aukawa tashar jirgin kasa ta Urumqi ne a ranar 30 ga watan Afrilu, inda suka tashi ababen fashewa 10, suka kuma rika sukar mutane da wukake. Daga bisani dai biyu daga cikin su sun rasu sakamakon fashewa da ta ritsa da su, yayin da kuma 'yan sanda suka cafke raguwar 8. (Saminu Alhassan)