in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a yi iyakacin kokari don tabbatar da lafiyar jama'a da dukiyoyin su
2014-02-13 15:25:55 cri
A ranar 12 ga wata da karfe 5 da minti 19 na yamma, an yi girgizar kasa da karfinta ya kai maki 7.3 a ma'aunin Richter, a garin Aqiang da ke gundumar Yutian a jihar Xinjiang mai cin gashin kanta.

Bisa kwarya-kwaryar labarin da aka samu, an ce, sabo da babu mutane sosai a wurin da girgizar kasa ta auku, ya zuwa yanzu ba a samu rahoton mutanen da suka rasu ko wadanda suka jikkata ba.

Bayan da aka yi girgizar kasa, sakatare jana na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasa Xi Jinping, ya dora muhimmanci sosai game da wannan batu, inda nan take ya ba da umurni ga sassan da abun ya shafa da su kara kaimi wajen tantance halin da ake ciki, su kuma gaggauta samar da taimako, da inganta sa ido game da girgizar kasar, don tabbatar da lafiyar jama'a da dukiyoyin su.

Mamban zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma firaministan kasar Sin Li Keqiang shi ma ya ba da umurni game da matakan da ya dace a dauka, wajen dakile tasirin girgizar kasar, tare da aikin ceton jama'a, inda ya bukaci da a gaggauta daidaita batutuwa, don magance sake aukuwar barna da bala'in ya haifar. Har ila yau ya bukaci a gudanar da ayyukan magance matsalar da girgizar kasar ta haifar, da tabbatar da ingantuwar zaman rayuwar jama'a, don tabbatar da zaman lafiya a zamantakewar al'umma.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China