Ya zuwa karfe 6 na dare a ran 14 ga watan Fabrairu, babu rahoton samun hasarar rayuka ko jikkatan jama'a, amma bala'in ya yi sanadiyyar lalacewar gidaje da dama, tare kuma da kashe dabbobi masu yawa, wassu gadoji sun fada, abin da ya kawo babbar asarar dukiya ga yankin He Tian.
Wani babban jami'in yankin He Tian ya bayyana a wannan rana cewa, bayan aukuwar bala'in, hukumar harkokin cikin gida na jihar ta dauki matakin tinkarar bala'i da ya dace cikin lokaci, tare kuma da samar da wasu kayayyakin tallafi cikin gaggawa, gami da tsugunar da wadanda wannan bala'in ya shafa su 85,676. Ya zuwa yanzu, an samu isashen tantuna, bargunan rufa, shinkafa da dai sauran kayayyakin yau da kullum, ban da haka, ana tafiyar da harkokin zirga-zirga, sadarwa, wutar lantarki, ruwan sha yadda ya kamata. An ba da labari cewa, jama'ar wurin sun samu kwanciyar hankali, al'umma na cikin natsuwa sannan ana zama rayuwa yadda ya kamata. (Amina)