in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana dukufa wajen gina gidaje masu inganci a jihar Xinjiang
2014-02-21 16:46:10 cri
Rahotannin daga ofishin kula da harkokin gidaje da raya birane na jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin, na cewa, tun daga shekarar 2011 zuwa karshen shekarar 2013, an zuba jarin da ya kai na yuan miliyan 74246 a jihar wajen gina gidaje masu inganci da yawansu ya kai dubu 920.9, inda mutane sama da miliyan 3.6 ke zaune a cikin wadannan sabbin gidaje masu dumi da iya jure girgizar kasa.

A kwanakin baya ne aka yi wata girgizar kasa mai karfin maki 7.3 a garin Yutian dake jihar, amma ba wanda ya rasu ko ya ji rauni, saboda galibin al'ummar jihar suna zaune ne a wadannan gidaje masu inganci.

Bugu da kari, a shekarar 2014, jihar Xinjiang za ta ci gaba da zuba jarin da ya kai kimanin Yuan biliyan 24 wajen gina sabbin gidaje masu inganci dubu 300 a jihar. (maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China