in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An ci nasarar binciken harin ta'addanci da aka kai gundumar Wushi da ke jihar Xinjiang ta kasar Sin
2014-02-17 11:04:35 cri
A ranar 16 ga wata, bayan da bangaren 'yan sanda ya yi bincike, an samu nasarar binciken shari'ar harin ta'addanci da aka kai wa 'yan sanda a gundumar Wushi da ke yankin Aksu a jihar Xinjiang ta kasar Sin.

Bayan da bangaren 'yan sanda ya yi bincike, ya gano cewa, harin da aka yi harin ta'addanci ne da aka kulla makirci sa don kai wa 'yan sanda. Yau da shekaru 3 da suka gabata, Mehmut Tohti ya fara yada tsattsauran ra'ayin addini tsakanin jama'a, lamarin da ya haddasa canja ra'ayoyin wasu mutane. Tun daga watan Satumba na shekarar 2013, mutane 13 da ke karkashin shugabancin Mehmut sun yi taron gangami, inda suka saurari tare da kallon shirye-shiryen ta'addanci ta hoton bidiyo, kana suka samu horo, don kafa wani rukunin 'yan banga. Daga watan Janairu na bana, wannan kungiya ta fara sayen motoci don kai harin, kuma sun kera wasu abubuwan fashewa da wukake, da gwajin wadannan abubuwan fashewa, da shirya kai hari ga motocin sintiri na 'yan sanda da ke tabbatar da zaman lafiya. A ranar 14 ga wata da misalin karfe 4 na yamma, wasu mambobin kungiyar sun tuka motocin da suka saya, dauke da wasu abubuwan fashewa, rike da wukake, don aikata laifi.

Ko da yake bangaren 'yan sanda ya yi nasarar cafke su tare da wasu abubuwan fashewa, da wukake da motocin da suka yi amfani da su don aikata laifin. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China