Bayanan da reshen hukumar samar da wutar lantarkin Sin na (SGCC) da ke yankin ya bayar, ya nuna cewa, a shekara ta 2013, wutar lantarkin da tashoshin samar da wutar lantarki ta hanyar makamashin iska, da ruwa da kuma hasken rana suka samar, sun zarce kilowatts miliyan 1,368, adadin da ya kai kimanin 1 bisa 3 na dukkan karfin wutan Xinjiang baki daya.
Adadin karfin tashoshin wutar lantarki ta hanyar amfani da karfin iska ya kai kilowatts miliyan 500, wanda ya ninka sau 9 a shekara ta 2009, yayin da adadin tashoshin wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana ya karu da kilowatts miliyan 227.1 daga sifiri a shekara ta 2010, kamar yadda rahoton hukumar SGCC, reshen Xinjiang ya bayyana a ranar Lahadi.
A shekara ta 2010 ne aka kaddamar da aikin hade yankin na Xinjiang da tashar samar da wutar lantarki ta yankin arewa maso yammacin kasar Sin, ta yadda za ta rika samar da wuta a sauran sassan kasar, inda aka yi amfani da kudaden da aka samu wajen raya yankin na Xinjiang. (Ibrahim)