Yawan shirye-shiryen taimakawa yankin He Tian na jihar Xinjiang a shekarar nan ta 2014 ya kai 123, shirye-shiryen da aka kiyasta za su lashe kudin Sin biliyan 1.3.
Rahotanni sun bayyana cewa za a yi amfani da wadannan kudade ne a bangarori shida, wato gina gidaje, da ayyukan al'umma, da kimiyya, da masana'antu, samar da manyan ababen more rayuwa, bunkasa kungiyoyin jama'a, da samar da horo. Ban da haka, za a dora muhimmanci sosai kan jarin da za a zuba kan ayyukan bunkasa rayuwar jama'a.
A yayin taron baiwa yankin He Tian taimako na wannan shekara da ya guda a ranar 25 ga wata a nan birnin Beijing, inda aka tabbatar da shirye-shirye 26 da za a ci gaba da gudanar da su, da kuma sabbin shirye-shiryen 97. Ministan ba da jagoranci da aiwatar da shirin baiwa yankin He Tian taimako, Mr Wang Zhaolong ya nuna cewa, a fannin ba da ilmi, za a mai da hankali ne kan horar da malaman da suke iya yin amfani da harsuna guda biyu, da samar da horaswa a fannin ayyuka.
Har wa yau Wang ya ce za a kara inganta horaswa domin taimakawa mutane wajen samun aikin yi, sannan kuma a dora muhimmanci kan horar da malamai, da likitoci, da masanan kimiyyar gona da sauransu. (Amina)