Mataimakin darektan ofishin samar da taimakon gaggawa na jihar Xinjiang, Zhao Yan ya bayyana cewa, bisa yanayin da ake ciki yanzu, mafi yawan gidajen da suka lalace tsoffi ne. Mataimakin shugaban hukumar kula da girgizar kasa ta jihar Xinjiang, Zhang Yong ya furta cewa, ya zuwa karshen shekarar bara, an kafa gidajen da za su iya jure girgizar kasa kimanin miliyan 3 a jihar Xinjiang, kuma ya zuwa yanzu kimanin kashi 80% na makiyayan jiyar sun samu damar zama a wadannan gidaje masu inganci.
Kawo yanzu, hukumar kula da harkokin jama'a ta jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta samar da kayayyakin ceto zuwa yankin da ke fama da bala'in cikin gaggawa, tare da tsugunar da mutanen da bala'in ya ritsar da su.(Fatima)