Binciken da 'yan sanda suka gudanar ya nuna cewa, daya daga maharan mai shekaru 39 da haihuwa dan asalin gundumar Zayar ne, dake kudancin jiahr na Xinjiang. Kuma a baya ma maharan su biyu, suna da hannu cikin wasu al'amura masu alaka da kaifin kishin addini.
Da karfe 7 da minti goma na almurun jiya Laraba ne dai maharan su biyu, suka tada wani abun fashewa a tashar jirgin kasan dake Urumqi, lamarin da ya haddasa mutuwar su tare da wani mutum guda.(Saminu)