Mr. Li wanda ya yi wannan alkawari gaban mahalarta taron tattalin arziki na duniya da ake gudanarwa kan Afirka a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya. Ya kara da cewa kamar ko da yaushe, Sin za ta dada agajin da take baiwa nahiyar Afirka, ba kuma tare da gindaya wani sharadi ba.
Kazalika Mr. Li ya ce kasar Sin a shirye take ta taimakawa kasashen Afirka wajen samar da ababen more rayuwa, da suka kunshi layukan dogo, da manyan hanyoyin mota, da habaka harkar sufurin jiragen sama. Ya ce za a baiwa sashen hadin gwiwa tsakanin sassan biyu, musamman a fannin samar da ababen more rayuwa cikakkiyar kulawar da ta dace. (Saminu Alhassan)