in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Najeriya za su zurfafa dangantakar siyasa
2014-05-08 22:02:27 cri
Wata sanarwar hadin gwiwa da mahukuntan Sin da Najeriya suka fitar a ranar Alhamis din nan, ta bayyana aniyar sassan biyu ta zurfafa dangantakarsu a fannin siyasa, ciki hadda batun fadada hadin gwiwa wajen tinkarar batutuwan shiyya-shiyya da na kasa da kasa.

Bugu da kari sassan biyu sun ayyana aniyar ci gaba da ziyara, da tuntubar juna, domin tabbatar da dorewar hadin kai da fahimtar juna tsakaninsu.

An dai cimma wannan kuduri ne a ci gaba da daddale yarjeniyoyi da firaministan kasar Sin ya yi da mahukuntan kasar, yayin ziyarar aiki da yake yi a Najeriyar.

Mahukuntan Najeriyar dai sun jaddada kudurinsu na marawa manufofin kasar Sin baya, yayain da bangaren Sin ke bayyana fatan ci gaba da tallafawa Najeriya wajen kare ikon mulkin kan ta, da tsaro da kuma bunkasar tattalin arziki.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China