Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ya bayyana a nan birnin Beijing a ran 28 ga wata cewa, Sin na maraba da matakan da Autsrilia ta dauka a kokarin da ta ke na laluben jirgin saman Malaysia da ya bace, Sin kuma za ta ci gaba da tura sojojinta domin shiga aikin neman jirgin a zagaye mai zuwa.
A yau Litinin 28 ga wata ne, firaministan kasar Austrilia Tony Abbott ya kira wani taro don sanar da shirin aikin laluben jirgin,inda ya nanata cewa, za a bayar da muhimmanci sosai kan aikin gano jirgin a karkashin ruwa.
A wani taron manema labaru da aka yi a wannan rana, Mr Qin ya nuna cewa, bayan aukuwar hadarin, bangarorin dake da alaka da wannan batu ciki hadda Sin, Malaysia, Austrilia da sauransu sun yi hadin gwiwa sosai wajen laluben jirgin saman, wanda ya zuwa yanzu aka kwashe fiye da kwanaki 50, a nata bangare, a kokarinta, Sin ta tura jiragen ruwan yaki 18, da nemi taimakon jiragen ruwan fasinja 66 da jiragen ruwan kamun kifaye 20, fadin sararin teku da suka gudanar da aikin laluben jirgin ya kai muraba'in kilomita miliyan 1.3. Ban da haka kuma, Sin ta tura jiragen sama da dama zuwa wurin, har ma ta yi amfani da tauraron dan Adam 21, abin da ya sa, ya zama aikin lalube mafi girma da Sin ta gudanar a cikin tarihinta. (Amina)