Mr Li ya yi bayanin a lokacin zantawar su cewa Sin ta tura jiragen ruwa fiye da 10, kuma jiragen saman kasar da dama suna yin hadin kai da sauran na kasa da kasa domin nema da gano duk wata shaida na abubuwan da ka iya nuna tarkacen jirgin ne.
Ban da wannan kuma, jiragen ruwan masu zaman kansu na kasar Sin wadanda suka ratsa wannan yanki da jiragen ruwan kamun kifaye 20 suma sun shiga aikin neman jirgin.
A ta bakin kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Hong Lei lokacin ganawar sa da manema labarai a nan birnin Beijing a safiyar yau ya ce kasar ta bayyana matsayin data dauka a game da kokarin da ake yi na neman jirgin saman da ya bace.
Kuma Kasar Sin zata cigaba da neman wannan jirgin saman da ya bace domin yYa zuwa yanzu kasar ta tura jiragen ruwan yaki 7 domin su cigaba da gudanar da aikin a kan teku.. (Amina)