in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojin tekun Sin na kokarin neman jirgin saman Malaysia da ya bace
2014-04-11 14:07:31 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei, ya gabatar da wani bayani, game da aikin neman jirgin saman Malaysia da ya bace, yayin taron manema labaru da aka saba yi a ran 10 ga wata. Inda ya ce, ya zuwa yanzu, ana kokarin neman akwatin nadar bayanan jirgin saman, inda sojin tekun kasar Sin ke iyakacin kokarin ba da taimako ga wannan aiki.

Ya zuwa karfe 12 na ranar 10 ga wata, cibiyar aikin ba da agaji a teku ta kasar Sin, ta jagoranci jiragen ruwan kasuwanci 63, da ke kaiwa da komowa a yankin tekun Indonesiya, da tekun dake yamma da Austriliya, wurin da ya kai fadin muraba'in kilomita 165401, domin neman jirgin.

A wannan rana kuma, jirgin saman sintiri na Austriliya mai suna P-3 Orion, ya jiyo wani amo daga kasan teku, kusa da jirgin ruwan yakin Austriliya mai suna Ocean Shield, wanda ake zato mai yiwuwa ne ya zamo daga akwatin nadar bayanan jirgin sama ne.

A nasa tsakoci, kakakin hukumar tsaron kasar Amurka Steve Warren ya nuna cewa, a ran 9 ga watan nan, Amurka ta tura jiragen sama biyu da ake kira P-8 Poseidon, domin gudanar da aikin lalube, kuma ta girke na'urorin bincike a kan jirgin ruwan yakin Austriliyan mai suna Ocean Shield domin sauraron amon akwatin nadar bayanan jirgin saman da ya bace. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China