Ko da yake, ana fuskantar mawuyacin yanayin sama, Sin na ci gaba da gudanar da aikin bincike domin gano jirgin sama na Malaysia wanda ya bace.
Wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin, kuma mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zhang Yesui ya gana tare da jajantawa iyalan wadanda 'yan uwansu suka bace a birnin Kuala Lumpur na kasar Malaysia. Yana mai cewa, ya zuwa yanzu, Sin ta yi amfani da tauraron Bil Adam guda 21, jiragen ruwa fiye da 10 da kuma jiragen sama fiye da 10, aka tura su wannan yanki da zummar yin iyakacin kokarin gano Sinawa da ma sauran mutanen da wannan hadari ya rutsa da su.(Amina)