in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Malaysia za ta gabatar da kwarya-kwaryar rahoto kan jirgin saman da ya bace , in ji firaministan kasar
2014-04-25 20:47:38 cri

Firaministan kasar Malaysia Najib Tun Razak ya shedawa manema labaru na CNN a ran 24 ga wata cewa, Malaysia ta riga ta gabatarwa hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman fasinja wani kwarya-kwaryar rahoto kan jirgin samanta da ya bace, kuma za ta bayyana shi a fili a mako mai zuwa.

Ban da haka kuma, Najib Tun Razak ya nuna cewa, wannan hadari ba a taba ganin irinsa ba a shekarun baya bayan nan, wanda ya sha bamban da hadarin jirgin saman kamfanin zirga-zirgar jiragen saman Singapore a shekarar 1997 da kuma na kamfanin zirga-zirgar jigaren saman Faransa a shekarar 2009. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China