in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba a samu sabon ci gaba wajen neman jirgin saman Malaysia da ya bace ba
2014-04-21 11:02:38 cri

A ran 20 ga wata da safe, hadaddiyar cibiyar da ke kula da aikin ceton jirgin saman Malaysia mai lamba MH370 ta kasar Australiya ta sanar da cewa, jirgin ruwa da ke aikin ceto a karkashin ruwa mai lamba 'Bluefin-21' ya riga ya gudanar da aikin ceto a rabin yankin da aka kayyade, amma bai samu kome ba tukuna. Cibiyar aikin ceto a cikin teku ta kasar Sin ta fayyace cewa, a ran 20 ga wata, jiragen ruwan kasar Sin sun dauki nauyin neman jirgin Malaysia a fadin teku da yawansa ya kai muraba'in kilomita fiye da dubu 20.

Hadaddiyar cibiyar Asustraliya ta bayar da wata sanarwa cewa, a ran nan da safe jirgi 'Bluefin-21' ya gama aikinsa karo na 7. Ya zuwa yanzu, jirgin ya riga ya gama aikin ceto a kusan rabin yankin da ake tsammanin akwai yiyuwar samun jirgin Malaysia, amma ba a samu kome ba. An riga an fara aikin ceto karo na 8.

Ya zuwa karfe 12 na safe na ranar 20 ga wata, yawan fadin da aka gudanar da aikin ceto bisa yadda aka tsara ya kai muraba'in kilomita 715,343.5. Cibiyar aikin ceto a cikin teku ta kasar Sin ta cimma matsaya da jiragen ruwa na kasuwanci da su yi aikin ceto daga yankin teku da ke Indonisiya da na yammacin Australiya masu fadin muraba'in kilomita 178,847. Amma har yanzu ba su samu kayayyakin da ke da nasaba da jirgin sama na Malaysia da ya bace ba. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China