Haka nan hukuma mai kula da harkokin teku ta kasar Austriliya, ta sanar a ran 26 ga wata cewa, an dakatar da aikin ceto saboda rashin kyawun yanayi, aikin da kasashe shida da suka hada da Sin, Austriliya, Amurka, da Newzealand, da Japan da kuma Korea ta kudu ke aiwatarwa.
A ranar 26 ga watan nan ne dai Firaministan kasar Malaysiya Tony Abbott ya bayyana cewa, an gano wasu tarkace a kudancin tekun Indiya. Sai dai abu ne mawuyaci a iya tabbatar da hakikkanin inda suke, a kuma fiddo su saboda yanayin da ake ciki, fadin wurin da kuma yanayin samaniya mai hadari.
A hannu guda kuma, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka Marie Harf, ta bayyana a ran 25 ga wata cewa, Amurka na tuntubar hukumomin lura da tauraron bil Adam, kan harkokin teku na kasa da kasa na Birtaniya, domin tattaunawa kan ra'ayin gwamnatin Malaysiya. Harf ta ce, Amurka za ta nazarci alkaluman da aka bayar, tare da nazartar ra'ayin da aka nuna dangane da lamarin. (Amina)