Ban da haka kuma, a safiyar ran 18 ga wata, an kammala jibge muhimman kayayyaki a cikin jirgin ruwan Hai Xun-01, kuma jirign ya tashi zuwa sararin teku dake yamma da Austrilia domin gano inda jirgin saman Malaysia yake, ana sa ran zai isa wurin a daddaren ran 21 ga wata ko safiyar ran 22 ga wata.
A nasa bangaren, fFiraminisan kasar Malaysia Najib Tun Razak ya gana da mambar hukumar siyasa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwamins Kwaminis ta Sin Hu Chunhua a fadarsa a ran 8 ga wata, inda ya nuna cewa, Sin sahihiyar abokiyar kasar Malaysia ce, kuma ya nuna matukar godiya ga taimakon da Sin ta baiwa kasar wajen daidaita wannan matsala. A nasa bangare, Mr Hu ya bayyana cewa, Sin na fatan kara hadin gwiwa da kasar Malaysia domin kara kokarinsu wajen gudanar da aikin laluben jirgin.
Dadin dadawa, cibiyar dake jagoranci jagorantar aikin lalube jirgin saman Malasiya ta Austrailia ta nuna a ran 18 ga wata cewa, na'urorinta ta kammala aikinta a karo na hudu a daren ran 17 ga wata, ba tare da gano wani abu ba. Kuma tuni aka fara aikinta karo na biyar.
Yanzu kuma ana mai da hankali kan yankuna sararin teku uku a ran 18 ga wata, wadanda fadinsu ya kai muraba'in kilomita 51870. An tura jiragen saman yaki 11 da jiragen ruwa 12 domin su gudanar da aikin lalube a wannan rana. (Amina)